Yayin da Musulmi a jamhuriyar Nijer ke cigaba da morewa wa kwanakin babbar sallah ta wannan shekara, kiristoci ne a kasar suka yi anfani da wannan damar domin nunawa duniya irin kyakkyawa dangantaka da yanda suke zaune lafiya lumi da 'yan'uwan su Musulmai, yayin da wadansu kasashe makwabtan Nijer din inda bambancin addini, ke rikidewa zuwa fada ko arangama ko ma abkawa jama'a babu gaira babu daliili a wuraren ibadar su.
Pasto Abubakar Musa shugaban gamayar darikokin addinin kirista na Birni N'Konni, yace sun taya musulmi murnar sallah da ma yin kira gare su, su yiwa kasar addu'a.
A nata bangaren, kungiyar CEDIR dake hada kan mabambanta addinai a Nijer, ta hanyar shugaban ta, tayi marhabin da wannan halaya na nuna da ma kara kawo zaman lafiya a kasar tsakanin Musulmi da Kiristoci.
A kowane lokaci, bangarorin kan taya juna murna da zummar shinfida tubali kyakkyawa na zaman lafiya a Jamhuriyar Nijer tsakanin mutanen da ke da bambancin addini.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: