Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ganawar Tinubu, Kwankwaso Ta Haifar Da Sabuwar Dambarwar Siyasa A Kano


Tinubu, Ganduje da Kwankwaso
Tinubu, Ganduje da Kwankwaso

“Ai kamata ya yi idan zai gan shi, mu ma ya kira mu, ko ba ka gane ba? sautin muryoyin da aka kwarmata ya bayyana Ganduje yana cewa.

Ga dukkan alamu dambarwar siyasar jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sake kunno kai – amma wannan karon a matakin tarayya.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da ganawar da aka yi tsakanin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da tsohon gwamnan jihar ta Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

A tsakiyar makon da ya gabata rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso ya kai wa Tinubu ziyara a Paris, babban birnin Faransa.

Wani sautin muryoyi da ya karade shafukan sada zumunta a karshen makon da ya gabata, ya bayyana yadda Ganduje yake amayar da korafinsa ga tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na wucin gadi a jam’iyyar APC, Ibrahim Masari kan wannan ganawa ta Tinubu da Kwankwaso.

Ibrahim Masari
Ibrahim Masari

Kafin ta tsayar da Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, Masari APC ta tsayar a matsayin dan takarar wucin gadi.

Shi dai Kwankwaso shi ya lashe zaben shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP a zaben na 2023.

Ya lashe kananan hukumomi 38 daga cikin 44 inda ya samu jimullar kuri’a 997,279.

Kazalika jam’iyyar ta NNPP wacce Kwankwason ke jagoranta, ita ta lashe zaben gwamna a jihar.

Masu lura da al’amuran siyasa na nuni da cewa, Tinubu na zawarcin Kwankwaso ne duba da cewa mulkin jihar ya koma karkashin jam’iyyar ta NNPP.

Sai dai kamar yadda tattaunawar ta Ganduje da Masari da aka kwarmata ta nuna, Gandujen ya ce rashin adalci ne a tsallake shi ana kokarin janyo Kwankwaso, duba da cewa ya yi wa jam’iyyar ta APC da ke shirin kafa sabon mulki hidima.

A tattaunawar, Ganduje ya nunawa Masari cewa haduwar ta Tinubu da Kwankwaso, an yi ta ne ba tare da an sanar da shi ba.

“Ai kamata ya yi idan zai gan shi, mu ma ya kira mu, ko ba ka gane ba? Ganduje ya ce.

“Ka dai ka yi hakuri,” Aka ji Masari yana rarrashin Ganduje.

Sai dai a martanin da ya mayar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, zababben dan majalisar Abdumumin Jibril wanda jigo ne a jam’iyyar ta NNPP, ya ce sai da Tinubu ya nemi ra’ayin Ganduje kafin ya gayyaci Kwankwaso.

Abdulmumin Jibril
Abdulmumin Jibril

“Sam ba a yi wa zababben shugaban kasa adalci ba idan aka duba yadda Gwamna Ganduje ya fito ya yi magana, duba da cewa, zababben shugaban kasa ya tuntube shi don ya ji ra’ayinsa kafin wannan haduwa, domin ni da kansa ya fada min.

“Ban yi tsammanin zababben shugaban kasa zai yi watsi da duk wani da ya mara masa baya ba…. amma dai abu muhim anan shi ne hadin kai da ci gaban kasa.” In ji Jibril.

Duba da yadda wannan al’amari ya dauki dumi, gwamnatin jihar Kano ta yi wuf ita ma ta mayar da martani kan wannan ka-ce-na-ce da ake ta yi.

Malam Muhammad Garba
Malam Muhammad Garba

“Wannan tattaunawa da ake ta yamadidi akanta, aikin wasu ‘yan barandan siyasa ne da aka biya suke kokarin sauya fuskar “tattaunawar da ake ikirari” da nufin haifar da rashin jituwa a tsakanin manyan ‘yan siyasar biyu” Kwamishinan Yada labarai Malam Muhammad Garba ya fada cikin wata sanarwa da ya fitar kamar yadda Trust ta ruwaito.

Ya kara da cewa, wasu mutane ne da ba su gamsu da yadda Tinubu, Ganduje da Masari suke dasawa ba ne, suke kokarin amfani da hanyoyin da za su haifar da rudani.

Yayin da ake ci gaba da wannan ce-ce-ku-ce, abin da ya rage shi ne yadda Tinubu zai kafa gwamnatinsa kuma su wa zai nada a mukamai daban-daban.

XS
SM
MD
LG