Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Rantsar Da Tinubu: Za A Killace Wasu Hanyoyin Birnin Abuja


Jami'an 'yan sandan Najeriya suna aikin ciro wayoyin saka shinge a Abuja. (Hoto:Facebook/Femi Adesina)
Jami'an 'yan sandan Najeriya suna aikin ciro wayoyin saka shinge a Abuja. (Hoto:Facebook/Femi Adesina)

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da zababben Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Hukumomi a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, sun ba da izinin rufe wasu hanyoyi da suka dangana da gine-ginen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar saboda faretin rantsar da sabuwar gwamnati da za a yi.

Za a rufe hanyoyin ne daga ranar Juma’a 26 ga watan Mayu da misalin karfe 2 na rana har sai ranar 29 ga watan Mayu kamar yadda rahotanni suka nuna.

A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da zababben Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Rahotanni sun ruwaito Sakatariyar walwala a ofishin ma’aikatan gwamnatin tarayyar Dr. Ngozi Onwudiwe a matsayin wacce ta sanar da shirin daukan matakin rufe wasu hanyoyin a birnin.

A cewar Mrs. Onwudiwe, umurnin rufe hanyoyin na da nasaba da matakan tsaro da kwamitin karbar mika mulki da shugaban kasa ya kafa ya dauka, don a tabbatar bikin ya gudana ba tare da wata tangarda ba.

Wasu kafafen yada labaran Najeriya sun ruwaito cewa ba za a bude hanyoyin ba sai ranar 30 ga watan Mayu, kwana guda bayan an kammala bikin rantsar da sabuwar gwamatin Tinubu.

Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairu, amma wasu manyan jami'iyyun siyasar kasar na kalubalantar sakamakon a kotu.

XS
SM
MD
LG