Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Sarauniyar Ingila Na Cika Shekaru 70 Kan Gadon Sarauta


 Sarauniya Elizabeth ta biyu yayin bukin murnar cika shekaru 70 a kan gadon sarauta.
Sarauniya Elizabeth ta biyu yayin bukin murnar cika shekaru 70 a kan gadon sarauta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna da fatan alheri ga mai martaba Sarauniyar Elizabeth ta biyu dangane da bikin murnar cika shekaru 70 a kan mulki.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, Sarauniya Elizabeth ta biyu ita ce Sarautar Burtaniya ta farko da ta kai shekaru saba'in akan gadon saraunta, a cewar wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Asabar da Muryar Amurka ta sami kwafin.

Shugaban ya bayyana Sarauniyar a matsayin shugaba mai aminci, mai kishin kasa, mai tausayi wadda ta yi wa al’umma aiki, ba wai a matsayin mai mulki ba, a matsayin abokiya da ‘yar uwa wadda kuma a yanzu ita ce wadda ta fi kowa dadewa a kan gadon sarauta.

Sanarwar ta tace, "Mutane ba sa daina amincewa da Sarauniya Elizabeth. Ƙarfin imaninsu shine cewa ko yaushe tana da damar iya bayarwa, musamman a lokutan wahala. Wannan tabbas gaskiya ne cewa Sarauniya Elizabeth koyaushe tana yin aiki kuma tana bayarwa bisa ga tsammanin mutane."

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa, "a yayin mulkin nata, inda a kwanan nan ta rasa mijinta kuma babban mai goyon bayan Yarima Philip, na Edinburgh, ni da dukkan 'yan ƙasarmu muna yi mata fatan ƙarin shekaru a matsayin Sarauniyar Ingila kuma Shugabar Commonwealth, cikin kyakkyawan koshin lafiya."

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG