Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zaman Makokin Mutanen Da Suka Mutu a Hatsarin Tankar Mai A Lokoja


Tankar Mai
Tankar Mai

Gwamnatin jihar Kogi ta ayyana zaman makoki na kwana 2 domin alhinin mutane kusan 30 da suka rasa rayukansu sanadiyyar hatsarin wata mota tankar mai a Lokoja, babban birnin jihar.

Hatsarin ya auku ne a ranar Laraba, sa'adda tankar da ke dauke da man fetur ta fadi ta kuma kama da wuta a garin Lokoja, lamarin da yayi sanadiyyar konewar mutane kimanin 30, mafi akasarinsu yara 'yan makaranta.

Kwamishinan Watsa Labarai na jihar ta Kogi Kensley Panwo, ya ce lamarin babban abin damuwa ne, ya kuma ce "gwamnati za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan al'amari."

Hatsarin motocin dakon mai a Najeriya abu ne da manazarta suka ce ya zama ruwan dare a kasar, lamarin da direbobin tanka din ke ta'allakawa da rashin kyan titunan kasar.

Faruku Muhammad Kawo, mataimakin shugaban kungiyar direbobin tanka a jihar Naija, ya ce rashin kyawawan hanyoyin mota ne ke haddasa yawan hatsura, musamman a Arewacin Najeriya.

Ya ce rashin ingantattun hanyoyi ke sanya direbobin daukar lokaci mai tsawo akan hanya, wanda kuma hakan kan haifar da rashin isasshen bacci, lamarin da kan jefa da yawansu a cikin hadurra.

A makon da ya gabata ma kungiyar direbobin ta yi barazanar dakatar da aikin jigilar mai zuwa Arewacin Najeriya, sadoda rufe wata hanya da gwamnatin jihar Naija ta yi saboda lalacewarta.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG