Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Kira 'Yan Najeriya Su Godewa Allah


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaba Muhammad Buhari wanda yayi sallah a garinsa Daura dake jihar Katsina ya kira jama'ar Najeriya da su godewa Allah saboda Ya arbarkaci kasar da damina mai kyau kuma ayyukan da gwamnati ta sa a gaba na cigaba kama daga yaki da cin hanci da rashawa zuwa samarda wutar lantarki

Yayinda 'yan Najeriya suka yi babbar salla a hali daban daban, wasu sun yi yanka wasu kuma basu samu sun yi ba, shi kuwa shugaban kasa a garinsa ya yi.

Bayan ya kammala Idi da kuma yanka da yayi a gidansas hugaban ya aikawa 'yan Najeriya da sako da ya shafi yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatinsa ta sa gaba akai..

Shugaban yace " Mu godewa Allah damina tayi albarka. Mutane su fahimci halin da muka samu kasarmu...Shekara goma sha shida da waccan jam'iyya da gwamnatoci guda takwas, da muka zo muka tambaya ko an yi tanadin wani abu babu"

"Yaya batun lantarki?" da kowa ke bukata babu. "Babu dogo, jirgin kasa. Babu hanyoyin mota. Babu sha'anin tsaro. Saboda haka muka ce to me aka yi da kudin? Babu wanda ya bamu amsa amma mun fara kama wadanda suka san yadda aka yi da kudin. Saboda haka mutane su godewa Allah. Boko Haram mun san yadda muka yi dasu. Su ma na Niger Delta zamu san yadda muka yi dasu". inji Buhari

Ya cigaba da cewa "Mun godewa Allah ya bamu damina mai albarka.... Su kara ba gwamnati goyon baya.... Zamu yiwa mutane adalci kuma wadanda suka zalunci kasa , ba za'a yiwa kowa sharri ba amma duk wanda aka samu yayi sata za'a ce ya maido" inji shugaban.

Ga rahoton Nasiru El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG