Taron wanda ya gudana a birnin Los Angeles, ya samu halartar manyan mutane daga nan Amurka da Najeriya da kuma wasu kasashen.
A shekarar 2011 ne aka kaddamar da mujallar ta LIFE & TIMES a birnin Los Angeles, da nufin zakulo hazikan ‘yan Najeriya da suke taka rawar gani a bangarorin rayuwa daban-daban- kama daga kasuwanci, aikin gwamnati da aikin jarida da sauran ayyukan da ke amfanan mutane da yawa.
A wajen kasaitaccen bikin na bana, mujallar LIFE & TIMES ta karrama shugaban sashin Hausa na Muryar Amurka da lambobin yabo guda biyu – daya a kan godewa a aikin jarida, sai kuma dayan akan sadaukarwa da ya yi wajen yiwa ‘yan Najeriya mazauna Amurka hidima shekara da shekaru.
Yayin da ake zayyano wasu bangarori na bajintar aiki da hidima da Aliyu Mustapha Sokoto ya yi kenan – inda mai jawabin ya ce a cikin sama da shekaru talatin da Aliyu Mustapha ya yi a Muryar Amurka, ya yi manyan hirrarraki da shugabannin kasashen Najeriya da Nijar da dama, da kuma tsohon shugaban kasar Ghana. Haka zalika ya yi aikin aikawa da rahotanni daga manyan tarukan kasa da kasa da suka hada da rantsar da shugaba Nelson Mandela da kuma ziyarori da shugabannin kasashen Afirka suka kai fadar white house.
Kazalika, mujallar ta jinjinawa Aliyu Mustapha kasancewarshi shugaban kungiyar Zumunta a Amurka na kasa na farko – wacce ke da rassa a fiye da jihohin Amurka 20. A lokacin shugabancin na shi, kungiyar ta bullo da tsarin tallafin karatu na ganin yara da iyayensu ba su da hali sun samu yin karatu a jami’o’in Najeriya da sauran manyan makarantu.
Bayan ya nuna godiya ga mawallafan mujallar bisa wannan karamci, shugaban sashin Hausa na Muryar Amurkan ya ce irin wannan taro, babbar hanya ce ta shawo kan matsalar sanya bangaranci ko addini a cikin lamurra a Najeriya.
Kafin bikin karramawar, mujallar ta LIFE & TIMES ta wallafa hoton Aliyu Mustapha Sokoto a matsayin babban hoton shafinta na farko a mujallar da kamfanin ya buga ta lokacin bazara 2022.
Magajin garin birnin Carson a California, ya kara wata karramawar akan wacce mujallar ta Life and Times ta yi wa Aliyu Mustapha, wanda ya samu rakiyar iyalan gidanshi.
Wasu mutane uku da suma mujallar ta karrama a wajen taron bisa gudunmuwar da suke bayarwa a bangarorin kwarewarsu, su ne Dr. Abike Dabiri-Erewa da farfesa Theresa Okafor da kuma Barrister Ogochukwu Onwaeze.
A lokacin da aka kaddamar da mujallar LIFE & TIMES a 2011, mawallafinta, Chike Nweke dai, ya ce bai kamata a ce sai bayan mutane sun gushe a doron kasa ne sannan za a rika tunawa da gudunmuwar da suka bayar lokacin suna raye ba.
Chike Nweke ya ce baya ga tunawa da gudunmuwar da ‘yan Najeriya ke bayarwa tun suna raye, mujallar ta Life and Times ta na kuma kokarin gyara mummunar fahimtar da kasashen duniya ke yiwa Najeriya sakamakon irin labaran da kafofin yada labarai na kasashen yamma ke bayarwa a game da kasar: