Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya gana da manyan jami'an gwamnatocin kasashen Qatar da Kuwait jiya Talata, a kokarinsa na dinke baraka tsakanin kasar Qatar da sauran kasashen yankin Gulf.
Makonni uku bayan da Saudiyya da wasu sauran kasashen Larabawa su ka kakaba ma Qatar takunkumin tattalin arziki da na diflomasiyya, Tillerson ya tattauna a birnin Washington DC da Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al Thani, Ministan Harkokin Wajen Qatar, wadda kawar Amurka ce sosai.
Babban jami'in na Amurka ya yi kiran da a yi zaman tattaunawa tsakanin kasashen na yankin Gulf da cewa hakan ne hanya mafi dacewa ta cimma maslaha a diflomasiyyance. To amma, Saudiyya da Bahrain da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa ba su nuna wata alamar niyyar janye jerin bukatu 13 da su ka gindaya ba, ciki har da bukatar Qatar ta takaita huldarta da kasar Iran ta kuma rufe gidan talabijin dinnan na Al Jazeera wanda kasar ta Qatar ke daukar nauyinsa.
Daga bisani, a jiya Talatar, Tillerson ya gana da Ministan Harkokin Wajen Kuwait mai kula da bangaren zartaswa, wanda kuma shi ne Mukaddashin Ministan Yada labarai, Sheikh Mohammed Abdullah Al-Sabah, inda ya jaddada goyon bayansa ga niyyar Kuwait ta shiga tsakani a takaddamar ta kasar Qatar da sauran kasashen yankin Gulf bisa jagorancin Saudiyya.
Facebook Forum