Wuta na kara ruruwa a cikin jam’iyar APC tun bayan cin zabe da sukayi, yanzu kuma hankalin kowa ya koma ne a kan wai shin suwa zasu zama shuwagabanni a majalisar dattijai da ta wakilai ne. Wannan shine abu da yafi daukar hankali a wannan lokaci da ake shirye shiryen rantsar da sabuwar gwamnati.
Wasu ‘yan siyasa sun nuna nasu fahimtar wadda suke ganin yakamata ace a wannan karon, yankin Arewa maso gabashin kasar yakamata ace sun fitar da shugan majalisar dattijawa, ganin cewar yakamata ayi la’akari da halin da kasar ta ke ciki. Don yakama ta a ba kowane bangare damar su samu wakiltaka, tunda shugaban kasa ya fito daga bangaren Arewa maso yamma, shi kuma mataimakin shi ya fito daga kudu maso yamma, to lallai abun da yafi kamata shine a bama yankin Arewa maso gabas itama damar su taba.
A wani bangaren kuma, wasu suna ganin wannan ba wani abune da yashafi uwar jam’iya ba, ta zabi wanda take so ya zama shugaban ba, wannan wani abune da su ‘yan majalisun yakamata su zaba ma kansu, a tabakin Sanata Bukar Abba Ibrahim, ya bayyanar da cewar su a majalisar dattawa da ta wakilai, ai ba yara bane don haka su yakamata su zabi wadanda suka chan chanta.
Shi kuwa Alh. Buba Galadima, yana ganin anbaro shiri tun rani, tunda ba’ayi wannan shawarar ina shugaban majalisa zai fito ba kamin zabe, to a wannan marrar da ake cikin kawai abun fata shine ayi kokarin samun fahimta a tsakanin ‘yan majalisun kamin ranar 6 ga watan Yuni.