Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewar annobar kwalara ta hallaka jumular mutane dubu 1 da 932 sa'annan wasu dubu 194, 897 sun harbu da ita a fadin duniya.
Sanarwar da ofishin hukumar mai kula da yankin gabashin Tekun Maditereniyan ya fitar tace, an samu barkewar annobar ne daga ranakun 1 ga watan Janairu zuwa 26 ga watan Mayun daya gabata.
An samu rahoton bullar annobar a kasashen duniya 24 a tsakanin yankunan da hukumar lafiyar ke kula dasu guda 5 inda tafi kamari a kasashen yankin gabashin tekun maditereniyan sai nahiyar Afrika dake biye masa, sa'annan yankin nahiyoyin Amurka da kasashen kudu maso gabashin Asiya sai kuma yankin nahiyar Turai.
Ba'a samu rahoton bullar annobar a tsakanin kasashen yankin yammacin tekun pacific a wannan lokaci ba.
Zuwa watan Maris din daya gabata, WHO tace ta karar da tarin allurar rigakafin annobar kwalara data tanadarwa duniya.
Saidai duk da haka tayi nasarar zarta adadin ko ta kwana data tanada na alluran rigakafi miliyan 5 a karon farko a farkon watan yunin da muke ciki.
WHO ta bada rahoton cewar kasashe 16 ne suka bukaci alluran rigakafin kwalara miliyan 92 tun a watan Janairun bara- adadin daya kusa ninka allura milyan 49 da aka samar a wancan lokaci.
Dandalin Mu Tattauna