Mashawarcin gwamnan Legas na musamman akan harkokin kiwon lafiya, Dr. Kemi Ogunyemi, ta bayyana cewar adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar, ya karu zuwa mutum 21, bayan rahotannin da aka samu a baya dake cewa mutum 350 ne suka kamu kuma 15 ne suka mutu.
Ta kuma kara da cewar adadin wadanda suka kamu da kwalara a fadin jihar ya karu zuwa mutum 401, inda cutar tafi kamari a yankunan Lagos Island da Kosofe da kuma Eti-Osa.
A yau Alhamis, Dr. Ogunyemi ta bayyana hakan lokacin da take bada karin haske game da annobar, bayan data gana da mambobin cibiyar bada agajin gaggawa a fannin kiwon lafiyar al’ummar jihar Legas.
Ta kara da cewar adadin wadanda cutar ta hallaka ya karu zuwa mutum 21, karin mutane 6 akan adadin da aka bada rahoto a baya.
A cewarta, an yi hasashen samun karuwar adadin sakamakon bukukuwan Sallar layya da aka yi, al’amarin dake janyo cunkoson jama’a a wuri guda.
Saidai tace, ana samun raguwar wadanda ke kamuwa da cutar a ilahirin kananan hukumomin jihar, musamman ma wadanda a da aka samu bullarta saboda daukar matakai da sanya idanu daga gwamnatin jihar.
Dandalin Mu Tattauna