Fadar White House ta fada jiya Lahadi cewa, ba za ta yi shaci-fadi ba kan ko Korea ta Arewa na shirin maido da ayyukanta na gwajin makami mai linzami.
Amma kuma Fadar gwamnatin ta Amurka, ta ki amincewa ta yi nazari kan hotunan tauraron dan Adam, da suka nuna cewa Pyongyang na hada sabon makamin roka.
Mai ba da shawara kan harkar tsaron kasa a Amurka, John Bolton, ya fada a shirin ABC News cewa, Amurka na sa ido kan Korea ta Arewan “akai-akai,” inda ya ce, “ni ba zan yi shaci-fadi kan wadannan hotunan tauraron dan Adam ba.”
A cewar shi, Amurka “na dogaro ne da bayanan” da tauraron dan adam dinta yake nuna mata.
Facebook Forum