Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Whatsapp Ya Sanar Da Wani Tsari Da Zai Bai Wa Masu Amfani Da Shi Damar Gyara Saƙonnin Da Su Ka Aika Da Su


Manhajar WhatsApp
Manhajar WhatsApp

Shahararrren kamfanin aika saƙo na nan take na WhatsApp, ya sanar da wani tsari da masu amfani da manhajar suka dade su na jira sosai, wanda zai bai wa masu amfani da shi damar gyara saƙonnin da suka aika da su.

Mark Zuckerberg, babban mamallakin na kamfanin Meta ya bayyana wannan sabon cigaban.

A wannan sabon fasalin, yanzu masu amfani da WhatsApp za su iya gyara saƙonnin da suka aika har bayan mintuna 15 bayan aika su.

Mark Zuckerberg
Mark Zuckerberg

A baya can, masu amfani dole ne su bi wasu hanyoyin kamar share saƙon ko sake aika saƙo na biyu a matsayin gyara. Fasalin gyarar saƙon ya na nufin samar wa masu amfani da manhajar Whatsapp karin iko a tattaunawarsu, ba su damar gyara kurakurai, yin bayani, ko ƙara muhimman bayanai cikin saƙonsu.

Manhajar Whatsapp
Manhajar Whatsapp

Cikin hanya mai sauki ake amfani da tsarin gyaran sako na Whatsapp, za su iya danna ko kuma riƙe takamaiman saƙon da suke son gyarawa. Menu zai bayyana, yana gabatar da zaɓi mai dauke da sakon "Edit." Sai a zaɓa wannan zaɓi, ana zaɓansa za a sami damar yin gyara abubuwan saƙo daidai biyan bukata.

An ƙirƙiri wannan aikin don haɓaka daidaito da tsabtar sadarwa, bai wa masu amfani damar gyara kurakurai ko samar da ƙarin bayani cikin sauri.

Aiwatar da fasalin gyarar saƙon yana nuna ƙudurin WhatsApp don haɓaka ƙwarewar mai amfani gaba ɗaya. Ta hanyar ƙarfafa masu amfani da manhajar ikon gyara saƙonnin da aka aika, WhatsApp yana da nufin magance matsalolin gama gari na kurakurai ko canje-canje a yayin tattaunawa a cikin manhajar.

manhajar whatsapp
manhajar whatsapp

Meta, babban kamfani na WhatsApp, ya nuna sha'awar sabon fasalin kuma ya jaddada cewa masu amfani za su sami ƙarin iko akan taɗi da gyara kuskuren haruffa.

An riga an fara fitar da fasalin gyarar saƙon, kuma tuni mafiya yawan masu amfani da manhajar sun fara cin moriyar wannan sabon fasali kuma kamfanin na Meta ya tabbatar da na bada jimawa ba dukkannin masu amfani da manhajar za su sami damar amfani da wannan sabon fasali.

Ya na da kyau a lura cewa sauran manhajoji na aika saƙo, kamar Telegram da Signal, sun riga sun ba da damar gyara saƙonni iri ɗaya ga masu amfani da su. Bugu da ƙari, masu amfani da manhajar Twitter wanda ake biya sun daɗe su na iya samun dama ga maɓallin gyara don yin canje-canje ga sakon tweets ɗinsu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG