ABUJA, NIGERIA - Wannan wani gagarumin ci gaba ne bisa la’akari a baya da ya takaita zuwa na’ura daya tal.
Da wannan fasalin, yanzu masu amfani da WhatsApp za su iya amfani da WhatsApp akan na'urori da yawa, ciki har da wayoyi, kwamfutar hannu, da kwamfutoci, ba tare da fita da dawowa a duk lokacin da suka canza na'urori ba.
Sabon fasalin a halin yanzu yana cikin gwajin beta kuma za a fitar dashi ga jama'a nan gaba kadan.
Hakan zai taimaka wajen habbaka hada hada da manhajar musamman ga masu amfani da na'urori masu yawa don sadarwa.
Amma kuma akwai kuma damuwa game da yuwuwar tasirin tsaro na wannan sabon fasalin, musamman dangane da sirrin bayanai na (end-to-end encryption)
Kamfanin na WhatsApp ya bayyana cewa ya aiwatar da karin matakan tsaro don tabbatar da cewa bayanan masu amfani da su sun kasance cikin aminci da tsaro a duk na'urorin.
Gabaɗaya, wannan sabon cigaba wani karin samun nasara ne ga manhajar tare da karin samun yawan masu amfani da ita nan gaba kadan saboda biyan bukata da kuma saukin da ke cikin manhajar ta Whatsapp.