Kamfanin Facebook ya gano bakin zaren matsalar katsewa da ta abka masa a ranar Litinin, lamarin da ya hana miliyoyin mutane da ke amfani da kafar a sassan duniya samun sukunin gudanar da huldodin da suke yi da shafin.
Katsewar wacce ta fara da tsakar rana (agogon Amurka) ta shafa har da Instagram da WhatsApp wadanda duk mallakin kamfanin na Facebook ne.
Masu bibiyar shafukan da dama a sassan duniya sun yi korafin katsewar shafukan, abin da ya sa kamfanin ya fito ya ba da hakuri.
Amma bayan sa’o’i shida al’amura sun daidaita inda kamfanin ya sanar da cewa an “maido da aikin shafukan akan duniyar yanar gizo.”
Masu bibiyar shafukan da dama a sassan duniya daga bayan sun bayyana cewa shafukan sun dan fara aiki.
Duk da cewa ya gyara matsalar, Facebook bai bayyana takamaiman abin da ya haifar da katsewar ba.
Wannan lamarin na faruwa ne yayin da wata mai kwarmata bayanan sirri ke shirin bayyana a gaban wani kwamitin majalisar dattawan Amurka don ba da bahasi kan zargin da wani rahoto ya yi, wanda ke cewa kamfanin na sane da irin illolin da Facebook yake yi wa mutane amma ba ya daukan matakan yin gyara.