‘Yan Nijer sun fara nuna damuwa a game da yadda manhajar wayar salula wato “whatsapp” ke kokarin haddasa kin yarda a tsakanin jama’a sakamakon lura da yadda wasu ke amfani da wannan kafa don yada maganganun da aka yi a asirce da nufin cimma wata muguwar manufa.
Yanzu haka wani jami’in fafutika, Nassirou Seidou na kungiyar La voix des sans voix na hannun ‘yan sandan farin kaya, inda aka yi ta yada muryarsa ta manhajar “whatsapp” yana bayyana shakku dangane da yiyuwar zabubukan da ya kamata a gudanar a shekarar 2020 da 2021 sanadiyar dokar ta-bacin watanni 3 da gwamnatin Nijer ta kafa a makon jiya da nufin dakile yaduwar cutar coronavirus.
Alhaji Nassirou ya yi wannan maganar ne a kebance ta manhajar “whatsapp” da wani abokin huldarsa amma kuma aka yi ta yada muryarsa a tsakanin jama’a.
Masanin tsarin zamantakewar al’umma Dr. Sani Yahaya Janjouna, ya ce ya kamata mutane su kula su kuma gyara tsarin zamantakewa.
Mutum na biyu da ya fada cikin irin wannan tarkon shine shugaban wani asibiti mai zaman kansa, Dr. Mala Tijjani wanda shi ma wasu abokansa suka fallasa hirar da suka yi ta manhajar “whatsapp” a cikinta yana mai nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin Nijer ke tafiyar da yaki da annobar cutar COVID-19, lamarin da ya sa aka tsare shi a ofishin ‘yan sanda.
Dr. Maina Karte, masanin tsarin mulki ne a Nijer, ya ce nisantar da kai daga yada wani abu dake kama da labarai a wajen mutanen da basu da masaniya akan ka’idodin yada labarai shine abin yi don kare kai daga shiga tarkon masu fallasa bayanan sirri.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum