A cikin hirarsu da wakilin sashen Hausa Nasiru Yakubu Birnin Yero, mallam Abbas Shehu jami’in tsare-tsaren kungiyar WRAPA a Kaduna, yace abinda yafi damunsu ba kawai abinda ya shafi tazarar haihuwa bane, amma abinda yafi damunsu shine abinda yake faruwa a wadansu lokuta inda ake tarar da mata a gidajensu ainda abubuwan da ya kamata a kula da su da ya shafi daukar ciki da kulawa da ita matar lokacinda ta dauki ciki da lokacin da zata haihu, da abinda take bukata bayan ta haihu da kuma shi kansa yaron, sai kaga mafi yawanci ba a kulawa da shi duk da yake addini ya bada damar kulawa da mata da abinda aka Haifa.
Mallam Shehu Abbas ya bayyana cewa haihuwa a gida yana da hadari domin idan aka sami matsala, yana da wuya a iya taimakonta idan ba a kaita asibiti ta sami kulawa cikin sauri yadda ya kamata ba.
Samun tazatar haihuwa tsakanin haihuwa na daga cikin abinda masana suka bayyana a matsayin daya daga cikin abinda ke sa mata koshin lafiya da kuma kaucewa mace-macen matan yayin daukar ciki da haihuwa.
Hira Da Shehu Abbas Kan Tazarar Haihuwa - 1:30