Doctor Rabiya tace mai haihuwa tana iya karuwa wajen haihuwa abinda zai sa ta rika zubar jinni. Tace Mata da suka haihu da yawa, sau biyar zuwa sama mahaifar tayi rauni, akwai yiwuwar zubar jinni,kuma mata masu haihuwar ‘yan biyu saboda girman ciki mahaifar ta dunkule bayan sun haihu zasu iya zubar jinni.
Tace hanyoyin da za a dauka wajen shawo kan matsalolin sune,mata su kiyaye idan suna da ciki. Farko ma mace ta kasance tana da isasshen jinni a jikinta lokacin da take da ciki kafin ma a kai ga haihuwa da za a yi zubar jinin domin idan tana da isasshen jinni a jikinta ko ta zubar ba zata tagayyara sosai ba. Amma idan bata da jinni sosai kafin ta haihu daga nan tayi zubar jinni zata iya mutuwa ta bar yaranta.
Awo yana da muhimmanci domin mata su san ko suna da isasshen jinni, ba wai sai sati biyu ko sati uku kafin su haihu ba, domin ta bude kati. Idan tayi zubar jinni a asibiti za a iya taimakawa wajen ceton ran mace mai ciki.
Idan mace ta sami zubar jini tana bukatar a kara mata jinni idan ba haka ba, kila zata mutu.
Wakilin Sashen Hausa ya yi hira da likitar a wajen taron lafiya da mata Musulmi suka shirya a garin Kaduna.