Mr. Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya yace rundunarsa ta cafke mutane biyar cikin mutane takwas da ake zargin su ne suka yi garkuwa da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Chief Olu Falae.
Kusan bayan awa 24 kacal da sanarwar 'yansandan ita ma hukumar 'yansandan farin kaya ko DSS a takaice ta ce ta cafke wasu mutanen daban bisa zargin su ne suka aikata yin garkuwa da Chief Falae.
Yayinda 'yansanda ke cewa sun damke nasu ne a jihohin Neja da Ekiti da Ondo ita kuma DSS ta ce ta cafke nata ne a jihar Kogi.
Da Muryar Amurka ta tammbayi kakakin 'yansandan ko basa aiki kafada da kafada tare da DSS sai tace zata yi magana ne kawai akan wadanda 'yansanda suka cafke. Tace amma babban sifetonsu ya tuntubi DSS da su basu wadanda suka kama domin su hadasu su kai kotu.
Amma Dr. Muhammad Dengel wani kwararre akan tsa'anin tsaro a Najeriya yana ganin babu hadin kai tsakanin hukumomin biyu. Babu kuma fahimmata tsakaninsu. Yace yakamata a zauna a dubi sha'anin tsaro a kasar.
Ga karin bayani.