Kwararru sun yi nuni da tashin tashinar dake faruwa a Najeriya da Mali da Niger da ma wasu kasashe a yammacin Afirka cewa alamu ne na rashin hadin kan shugabannin kasashen yankin, musamman a lokacin da suke fuskantar kalubalen tsaro. Wata da ta wakilci kungiyar Clean Foundation a taron ta ce sun gudanar da bincike a kasashe bakwai na yankin dangane da yadda jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu a lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro. Ta ce sun bayyana bincikensu da dabarun da yadda za'a iya yin anfani da su.
Shi kuma Abdulrahaman Idrisa kwararre a harkar siyasa daga kasar Niger ya bayyana damuwarsa ne akan yadda tashe-tashen hankali ke shafar kasarsa saboda halin makwaftaka. Ya ce rikicin dake shigowa Niger sun samo asali ne daga kasashen dake kusa da Niger ne irin su Mali, Arewacin Najeriya, da Libiya da ma wasu kadan daga kasar Algeriya. Rikice-rikicen dake faruwa a wadannan kasashen suna shafar Niger kuma basu san yadda zasu yi ba domin babu hadin kai a tsakanin kasashen yadda ya kamata.
An yi nazari a kan dabarun da ECOWAS ta dade tana bi wajen shawo kan tashin hankali da misalin yadda kungiyar ta kirkiro ECOMOG da AFISMA.. Dr Huseini Abdu na kungiyar Action Aid a Najeriya yana cikin kwararru da suka yi nazarin. Ya ce yadda jami'an tsaro suke yin anfani da makamai tamkar kamar sun fi karfin dokar kasa ya sa ya zama wajibi a zauna a zana tsarin aikinsu kana a fahimtar da su jami'an tsaron. Wajibi ne a kara masu ilimi a wayar da kawunansu dangane da abun da aikinsu ya kunsa da yadda zasu gudanar da shi. Yakamata su san aikinsu na da kwakwarar alaka da hakin mutum da tsarin mulkin kasa. Yakamata a sanar dasu cewa tsarin mulkin kasa shi ya basu aikin da suke yi kuma ya kamata su yi aikin yadda zai karfafa kasa ya kuma kare jama'arta. Dole su tabbatar cewa kowane dan kasa an biya masa hakinsa.
Jawabin bayan taro ya jaddada mahimmancin horas da jami'an tsaron da yi masu nasiha a kan bin umurnin dokokin kasashe a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
Ga karin bayani.