Hukumomin kasar na ganin wannan yunkurin ne zai kai ga samun mafita wurin dakile wannan cutar da kan yi sanadiyar asarar rayukan yara da dama a cikin kasar ta jamhuriyar Kamaru.
Wayar da kan jama’a ta kafafen yada labarai a yankin Adamawa, shine babban burin ma’aikatar kiwon lafiyar Kamaru game da yaki da cutar tsutsar ciki da ta sa yara da matasa a gaba a kasar. Allurar rigakafi itace hanya daya tilo da ma’aikatar ta runguma domin ceton rayuwar matasan.
Daya daga cikin iyayen yaran da suka je inda ake allurar rigakafin ya ce lallai wannan mataki da gwamnati ta dauka zai taimakawa iyayen yara musamman marasa galihu. Ya kara da cewa suna fama da rashin ruwan sha mai tsafta kuma haka na dalilin ziyartar asibiti akai-akai, amma wannan allurar rigakafin za ta kare ‘ya’yan su daga wannan cutar da zata yi sanadiyar zuwa asibiti.
Masana sun tabbatar da amfani da ruwa marar tsafta da abinci da ba a wanke sosai ba, shine ke janyo cutar tsutsar ciki.
Wata Malamar lafiya Miss Delphine ta bayyana abin da wannan aikin allurar ke kokarin cimma.
Ta ce “Burin mu ne mu yiwa yara dubu dari biyu wannan allurar rigakafin kafin nan zuwa karshen wata mai zuwa, muna kuma so kafafen watsa labarai su taimaka mana da isar da wannan sako lungu da sako har iyayen yara su je kuma su kawo yaran su a yi musu alluarar rigakafin."
Yaro da ya kamu da wannan cutar yana samun raunin jiki, baya iya yin komai, baya iya zuwa makaranta balle kiwo ko noma domin taimakawa iyayensa. Ko shakka babu wannan cuta na yin illa ga lafiyar raya daga shekaru 5 zuwa 14.
Ga rahoton wakilin mu Mohammadu Rabi'u daga Kamaru: