Hukumar Raya Yankin Tafkin Chadi ta ta ce ta himmatu wajen farfado tare da inganta yankin da ke fama da tarin matsaloli da suka hada da na tsaro, sauyin yanayi da karancin ruwa da abinci da dai sauransu, hakan na zuwa ne yayin wani babban taron kasa da kasa wanda a karon farko aka gudanar da irinsa a Najeriya.
A jawabinsa na bude taron, mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kiran da a hada kai wajen samar da zaman lafiya a yanki na Tafkin Chadi da matsalolin rashin tsaro da na sauyin yanayi ke zama babban cikas ga rayuwar mazaunan yankin
Ya ce ’’Hadin gwiwa da hadin kai tsakanin kasashenmu, tare da masu ruwa da tsaki a fadin yankin da kasashen yankin sahel, su ne muhimman hanyoyin tabbatar da tasirin ayyukan samar da tsari na farfado da tattalin arziki da zaman lafiya a wannan yankin’’
Hukumar, wacce ke samun tallafinta daga Babban Bankin Duniya da nufin shawo kan tarin matsalolin da suka mamaye yankin na Tafkin Chadi, ta bayyana cewa ta na aiki tukuru wajen ganin an cimma wannan buri. Ambasada Mamman Nuhu, Babban Sakataren hukumar ya jaddada muhimmancin daukar matakan. Shi ma Babban Shugaban Kungiyar Gwanoni na Kamaru a yanzu kana Gwamnan Arewa Mai Nisa ta kasar, Mijinyawa Bakari, ya bayyana hadin gwiwar dake tsakanin Najeriya da Kamaru kan batun, wanda ya ce hadan na da matukar muhimmanci.
Ita Amina Wali dake aiki a shirin farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya ta yi kari da cewa ya kamata a karfafa duk wadannan cibiyoyi na habbaka wannan yankin da ya sha fama da matsaloli iri iri.
Hukumar Cigaban Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya ta bayyana cewa samun nasarar aiki na bukatar makudan kudade tare da fatan dorewar aikin hadin kai tsakanin kasashe hudu na Tafkin Chadi da suka hada da Najeriya, Nijar, chadi da Kamaru, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar Farfesa, Bobboi Umar ya bayyana
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya: