Da ya ke bayani ma wakilinmu da ke Kaduna Lawal Isah Ikarah, babban Sakataren kungiyar Dr. Khalil Aliyu Abubakar ya yi takaicin yadda ya ce bayan kashe dinbin kudi ba tare da an ga sakamakon kirki ba, ana kuma gallaza ba wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Ya ce an kewaye yankin na arewa maso gabashin Nijeriya da jami’an tsaro amma duk da haka sai ka ji ana ta kai hare-hare. Ya ce to ko aljani ne ke kai harin? Don haka ya yi kira ga hukumomi da su yi la’akari da cewa tsarinsu da mishkila.
Dr. Khaleel ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su rinka mutunta al’adun mutane da addinansu a yayin gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro. Ya ce kamata ya yi jami’an tsaro su rinka tuna cewa bin abu cikin lalama da siyasa ya fi duk wani amfani da karfi da barazana da kuma tursasawa.