Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mai Baiwar Zane-Zane Ta Yi Amfani Da Baiwar Wajen Karrama 'Yan Kwallo


SOCCER-WORLDCUP/PARAGUAY-ART
SOCCER-WORLDCUP/PARAGUAY-ART

Wata mai baiwar zane-zane ‘yar kasar Paragua, wadda fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina Lionel Messi ya yaba baiwarta, tana baje kolin aikinta a Qatar inda ake gasar cin Kofin Duniya.

Tana amfani da kwallo wajen yin zane-zanen da take karrama ‘yan wasa, kamar fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Brazil, Pele. Yayinda gasar cin Kofin Duniya ta dauki hankalin masu sha’awar kwallon kafa , wannan kuma ya karawa Lili Cantero kwarin guiwa, wadda ta ke amfani da zane- zane wajen nuna irin kyaun da wassan ya ke da shi.

Lili tana karrama kungiyoyin kwallon kafar da su ka ci Kofin Duniya ta wajen yin zane-zane kan kwallon a wajen gasar cin Kofin Duniya.

DEP-FUT MUNDIAL BALONES-ARTE
DEP-FUT MUNDIAL BALONES-ARTE

Lokacin da Cantero ta ji labarin rashin lafiyar dan fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Brazil Pele dan shekaru 82, sai ta tsaida shawarar amfani da baiwarta wajen karrama mutumin da aka dauka a matsayin wanda ya fi fice a fannin wasan kwallon kafa.

Cantero ta fara tunanin hada amfani da baiwar da take da ita a fannin wasanni, lokacin da abokanta su ka roke ta ta yi masu zane zane a takalman kwallon kafar su.

DEP-FUT MUNDIAL BALONES-ARTE
DEP-FUT MUNDIAL BALONES-ARTE

Kafa hoton takalmin da Cantero ta yi mashi zane a kai da Messi ya yi, ya karrade kafafen sada zumunta ya kuma dauki hankalin gwamnatin Paraguay da ya sa ta tura ta Qatar domin baje kollinta.

Banda zanen da ta karrama Pelé, an kuma baje kolin samfarin zane-zanen Cantero a dakin baje kolin kayan wasan kwallon kafa na kungiyar kwallon kafa ta Amurka a Doba, da ya hada da kwallayen da aka karrama fitattun ‘yan wasan kwallon kafa kamar zanen dan wasan kwallon kafa na Argentina, Diego Maradona.

DEP-FUT MUNDIAL BALONES-ARTE
DEP-FUT MUNDIAL BALONES-ARTE

Cantero ta bayyana cewa, ta dade tana mafarkin nuna baiwar ta a gasar cin Kofin Duniya, kuma kwalliyarta ta biya kudin sabulu, mafarkinta ya cika.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG