Hukumar Nazarin Yanayin Karkashin Kasa ta Amurka ta ce wata girgizar kasa mai karfin maki 6.8, ta auku kusa da gabar arewacin chile da safiyar Yau Talata.
Kafafen yada labarai na cikin gida sun ruwaito irin barnar da girgizar ta fara yi.
An bayyana cewa an fitar da mutane da dama wadanda ke zama a wurin da lamarin ya faru a matsayin kandagarki, duk da dai ba a samu bayanai masu cewa akwai wanda ya samu raunuka ba.
Tuni girgizar kasar ta haifar da hucin girgiza har fiye da dozin guda.
Jami’ai a chile sun ce girgizar ba za ta iya haifar da ambaliyar tsunami ba.
Facebook Forum