Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsaurara Tsaro A Majalisar Jihar Kogi


Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Hon Alfa Imam, yace sune suka gayyaci jami’an tsaro a majalisar dokokin jihar domin tabbatar da tsaron.

Tun bayan tsige tsohon kakakin majalisar jihar Kogin, Hon Mamman Jima, majalisar jihar ta shiga cikin halin rudani, sabon kakakin majalisar dai yace basa bukatar majalisar kasa ta shiga cikin al’amarin majalisar dokokin, ya kuma ce wannan daliline ya sa suka garzaya kotu domin hana majalisar kasar shiga cikin lamarin.

A yanzu dai bangaren da ke adawa da sabon kakakin su kai goma sha uku daga cikin mambobi ashirin da uku na majalisar, Hon Godwin Ojo, na cikin yan majalisar dake adawa da sabon kakakin, a lokacin da yake mayar da martani kan maganar zuwa kotu da sabon kakakin yace sun garzaya, Ojo yace ga guri ga mai doki.

Domin jin ta bakin jami’an yan sandan jihar kan wannan batu wakilin Muryar Amurka, yayi kokarin jin ta bakin su amma hakan ya ci tura.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG