Farkon shigowar gwamnatin Muhammad Buhari sai da ta kaiwa jihohi doki domin samun biyan ma'aikata albashin wata da watanni da ma'aikata ke bin gwamnatocin bashi.
A wasu jihohin ma albashi kawai aka biya babu alawus alawus saboda matsalar rashin kudi. To saidai wasu masu kula da lamuran sun ce wasu jihohin basu yi anfani da kudin da gwamnatin tarayya ta basu ba a matsayin tallafi na biyan albashi.
A birnin tarayya Abuja gwamnatin birnin ta ware nera biliyan daya da miliyan dari shida ko N1.6b da ta rabawa kananan hukumominta shida domin biyan albashin ma'aikata na watanni biyu.
Muhammad Musa Bello ministan birnin yace tallafin kudin ba kyauta ba ne. Tallafin domin su biya albashin wata biyu ne kana daga bisani za'a dinga cire kudin daga kudadensu na shiga har su gama biya. Yace zasu gyara alamuran shugabanci da kuma gudanar da ayyukan gwamnati a kananan hukumomin shida domin a tabbatar kowa ya yi aiki a karshen wata zai samu albashi.
Teri Henry Isaac shi ne shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi na birnin Abuja yace sun ji dadin tallafin domin duk da rage hanya ne saboda matasalar an shigeta ne tun shekarar 2013. Yace an soma biyansu a makare har ta kai inda suka daina samun albashinsu tun watan Yunin bara.
Ga karin bayani.