Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Fansho A Jihar Bauchi Na Zanga Zangar Rashin Biyansu Kudadensu


Naira
Naira

A jihar Bauchi yan fansho sunyi dirar mikiya a sakatariyar gwamnatin jihar, inda suka toshe ofisoshin ma'aikatan fansho suka hanasu fitowa da zummar ganin sai gwamanati ta biyasu kudadensu da suke bi bashi har na kimanin watanni biyu zuwa uku.

Cikin jihar akwai masu karbar kudin fansho har kimanin mutane dubu shida. A lokacin da suke wannan zanga zanga wakilin Muryar Amurka dake jihar Abdulwahab Muhammad, ya ziyarci sakatariyar inda ya ganewa idanunsa yadda wannan bore ke tafiya.

Yan fanshon dai sun nuna rashin jin dadinsu ga gwamnatin jihar kan gazawarsu wajen biyan kudadensu na tsawon watanni biyu zuwa uku. A cewar wasu yan fansho, halin da suka shiga babu dadi kuma suna kira ga gwamtanin jihar da ta tarayya da su dauki matakin da ya kamata domin warware wannan matsala.

Mataimakin shugaban masu karbar fansho na kasa mai wakiltar jihar Arewa, yayiwa yan fanshon jawabi inda yace an kafa kwamiti domin a fara tantance masu karbar fanshon amma shugaban kwamiti din bai je taron ba, don haka babu wata tabbatacciyar magana kan yadda zata kasance.

To sai dai kuma a halin da ake ciki gwamnan jihar Bauchin Abdullahi Mohammad, baya Najeriya. haka kuma wakilin Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin gwamnatin jihar amma yaci tura.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG