Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Yara Da Matasa 30 Ne Suka Mutu A Gombe Sanadiyar Bullar Wata Cuta


Asibitin Yara
Asibitin Yara

Al ‘ummar yankin karamar hukumar Nafada a Jihar Gombe suna fuskantat wani yanayi mai tsoro da fargaba sakamakon bullar wata cuta da ta lakume rayukan yara da matasa sama da talatin.

GOMBE, NIGERIA - Cutar wadda ta fara kunno kai a cikin farkon watan Fabrairun wannan shekarar da muke ciki, ta na da alamun zazzabi da ciwon ciki, da ciwon kafa da kuma amayi kamar yadda bincike ya nuna.

Bayanai daga babban asibitin garin Nafada ya nuna cewar an kai samfurin cutar guda ashirin kuma sakamakon guda goma sha daya ya nuna cewar ba cutar Sankarau bane kamar yadda ake hasashe da farko.

Hakazalika bisa bayanan da suke da shi akwai mutane guda bakwai da suka rasu a wajensu, sauran mace-macen da basa da kididdigarsu sun faru ne a cikin gari.

Sakataren Gudanarwa na Babban Asibitin garin Nafada, Mr. Kefas K. Silanda, yayi karin bayani da kuma tabbatar mana da yanayın cutar, adadin wadanda suka mutu a asibitin da matakan da likitoci suka dauka na gwajin sanfurin cutar.

Daga bisani Muryar Amurka ta kai ziyara gidan wani wanda aka masa rashi sakamakon cutar, inda ya shaida mana cewa ‘yarsa ta fara rasuwa a farkon wannan watan na Maris, yanzu kuma ‘dansa ya rasu.

Ya kara da cewa kwata-kwata ciwon idan ya kama yara baya wuce sa’o’i 48 sai mutuwa.

‘Dan Majalisar Dokoki mai wakiltar Nafada ta Arewa Muhammed Tahir, ‘Dan Galadiman Nafada, ya ce bisa rahotan da aka ba shi, mutane sama da talatin ne suka mutu a sanadiyar cutar.

Wani mahaifiyin yara guda biyar ya ce a dole ya hana yaransa zuwa makaranta don bai san abun da zai faru ba.

Kamar yadda bayanai suka nuna cutar ta fara bayyana ne a wata makaranta a cikin garin na Nafada dake jihar Gombe.

Saurari cikakken rahoto daga Abdulwahab Muhammad:

Wata Cutar Da Ta Bullo A Jihar Gombe Ta Kashe Yara Da Matasa Akalla 30.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG