Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Lafiya Da Kwararru Sun Isa Kauyen Majema Don Shawo Kan Barkewar Cutar Zazzabin Lassa


Likitoci da kuma kwararru daga Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya, da kuma jami'an bada agajin gaggawa sun isa kauyen Majema dake karamar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe, don gudanar da binciken kwakwaf a gidaje, a wani yunkuri don shawo kan zazzabin Lassa fever da ya kunno kai a yankin.

An samu rahoton bullowar cutar bayan daya kama wani yaro mai shekaru takwas da haihuwa, kafin kuma daga baya wani rahoto ya fito na cewa wata yarinya yar uwar yaron itama anga alamun cutar a jikinta.

Dakta Joshua Abubakar shine darektan kula da lafiyar al'ummar jihar Gombe, yayiwa wakilin Muryar Amurka Aabdulwahab Muhammad karin bayani a wata tattunawar da su kayi ta wayar tarho jim kadan bayan da suka isa kauyen.

Inda yace sun sami mutanen garin sun kuma wayar musu da kai alokacin da wata ganawa da mutanen, bayan da suka yi ma mutanen bayanin cutar ne sai wani mazaunin garin ya daga hannu yace lalle akwai ‘dan sa da yake da duk alamun da suka fada, daga nan kuma suka ‘dauki yaron zuwa Gombe, domin bashi kulawar da ta kamata.

Yanzu haka dai an dauki jinin yaron don zuwa a auna, kuma a tabbatar da cewa yana dauke wannan cuta. bayan haka dai an tura jami’an lafiya zuwa gida gida domin wayarwa da mutane kai da kuma neman wadanda ke dauke da cutar.

Ga hirar Abdulwahab Mohammed da Dakta Joshua Abubakar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG