Idan aka duba jihohin Sokoto da Kaduna da Gombe adadin masu zuwa Asibiti a kullum domin cutar Maleriya na da yawa. Wakilin Muryar Amurka a Sokoto, Murtala Faruk Sanyinna, ya bada tabbacin cewa mutane na yin amfani da ganyen Gwanda da Darbejiya da sauransu don maganin cutar kamar yadda rahotan ya nuna.
Dakta Ahmad Gwama, shine shugaban hukumar lafiya matakin farko na Gwambe, ya tabbatar da cewa fiye da cewa kullum fiye da mutane 100 kan shiga babban Asibiti a jihar, don neman maganin Maleriya, ya kuma ce sun bi gadaje sun raba maganin gidan sauro, sai babbar matsalar da ake fuskanta itace har yanzu wasu mutane basu gane amfanin gidan Sauron ba, saboda da yawa idan aka rabawa mutane domin su shiga da iyalansu su kwanta, wasu sai suyi amfani da shi a lambunsu da ke bayan gida.
Dakta Nasiru Gwarzo, babban jami’i ne na ma’aikatar Lafiya ta Najeriya, dake nazari kan wannan cuta ta Maleriya. Yace ya kamata jama’a su fahimci cewa yanayin da ake ciki na karshen Damuna shine ya haddasa yaduwar Saurayen. Hakan ke nuna ya zama wajibi jama’a su rika kawar da ruwa mai kwanciya da amfani da gidan Sauro da magungunan feshi don rigakafin cutar.
Domin karin bayani.