Wadanda suka kamu da cutar na nuna alamu masu kama da mura, ciki harda zazzabi mai tsanani da matsanancin ciwon kai, kamar yadda mataimakin gwamna a gundumar Kwango, Remy Saki da ministan lafiya na lardin, Apollinaire Yumba suka bayyana a jiya Litinin.
An tura tawagar jami’an lafiya zuwa cibiyar kiwon lafiya ta Panzi domin daukar samfura tare da gudanar da bincike domin gano cutar.
Halin da ake ciki na kara haifar da damuwa kasancewar yawan mutane dake kamuwa da cutar na cigaba da karuwa, kamar yadda jagoran kungiyar fafutukar farar huka Cephorien Manzanza ya shaidawa Reuters.
“Cibiyar kiwon lafiya ta Panzi ta karkara ce, don haka akwai matsala wajen samar da magunguna,” a cewar manzanza.
Masu fama da cutar na mutuwa a gidajensu saboda kulawa, a cewar Saki da Yumba.
Wani masanin annoba a yankin yace cutar tafi addabar mata da kananan yara.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna