Wani rahoto na hukumar lafiya ta duniya na shekarar 2015, ya nuna cewa a kalla mutane miliyan dari biyu da gama sha hudu suka kamu da cutar cizon sauro ko malaria a turance cikin shekarar data gabata, kuma an sami rasuwar jama’a da suka kamu da wannan cuta har kimanin mutane miliyan dari hudu da talatin da takwas.
Koda shike rahoton ya nuna raguwar masu kamuwa da wannan cuta a duniya, amma a nahiyar Afirka lamarin ya sha bam-ban, domin kuwa ana samun karuwar masu kamuwa da wannan cuta ne, wadda ke hallaka jama’a akai-akai, kuma akasari kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.
Karuwar masu amfani da maganin cutar cizon sauro ko malaria a duniya yasa ake ci gaba da samun magungunan jabu wadanda ke haifar da mummunar illa ga masu amfani da maganin, ta dalilin haka ne a wannan mako gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi al’ummar kasar su kiyayi shan wani magani mai suna Quinine sulphate, wanda akasari ake samunsa a kasar Kamaru da kuma Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo.
An sami tabbacin cewa magungunan basa aiki yadda ya kamata, a wata sanarwa da jami’ar yada labarai a ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta fitar Mrs Bode Akinola, ta gargadi al’ummar Najeriya gabaki daya su guji amfani da maganin zazabin cizon Sauron mai suna Quinine Sulphate, wanda ake ganin zai iya shigowa Najeriya a kowane lokaci daga yanzu, ta ce da zarar anga irin wannan magani a garzaya cibiyar lafiya mafi kusa domin kai rahoto.
A can baya gwamnatin Najeriya ta fito da wani shiri na bayyana wasu lambobi a jikin magungunan zazzabin cizon sauro inda aka bukaci duk wanda ya sayi wannan magani, ya aika da wasu lambobin sirri zuwa ga wata lambar waya domin tabbatar da sahihancin maganin inda zai sami sakon cewa maganin yana da kyau.