Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Rudani Kan Ficewar Shekarau Daga PDP


Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau (Hoto: Shafinsa na Twitter)
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau (Hoto: Shafinsa na Twitter)

“Har yanzu ina @officialPDPNigeria, ana ci gaba da tuntubar juna, mai girma #IbrahimShekarau, Sarudaunan Kano na musanta ficewa daga jam’iyyar PDP.” Shafinsa na Twitter ya bayyana.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim shekarau, ya ce bai fice daga jam’iyyar PDP ba kamar yadda rahotanni ke nunawa.

A yau Talata, mai ba Shekarau shawara kan harkokin yada labarai, Sule Ya’u Sule ya fito ya bayyana rashin gamsuwarsu da abin da ya kira “rashin adalci" da ake masu daga hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja a hirar da ya yi da wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari.

Rahotanni da dama sun ruwaito Sule yana mai bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar bisa wannan dalili.

Amma shafin Twitter na tsohon gwamna Shekarau ya nuna cewa bai fita daga jam’iyyar ta PDP ba.

“Har yanzu ina @officialPDPNigeria, ana ci gaba da tuntubar juna, mai girma #IbrahimShekarau, Sarudaunan Kano na musanta ficewa daga jam’iyyar PDP.” Shafinsa na Twitter ya bayyana.

Reshen jam’iyyar ta PDP a kano ya fada cikin rudani, tun bayan da tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga APC ya koma jam’iyyar a watan Yuli.

Hakan ya haifar da takaddamar shugabancin jam’iyyar ta PDP tsakaninsa da Shekarau da Kwankwaso, lamarin da ya kai hedkwatar ta PDP daga Abuja ta rusa shugabannin jam’iyyar.

Bayan haka, an kafa kwamitin rikon kwarya mai dauke da mutum bakwai, matakin da bai yi wa bangaren Shekarau dadi ba.

Bangaren su Shekarau da Aminu Wali sun nuna korafi bayan da aka nada wani na hannun daman Kwankwaso a matsayin shugaban kwamitin rikon kwaryan.

Sannan mutum biyar cikin bakwai na mambobin kwamitin duk makusantan Kwankwaso ne, lamarin da ya sa bangaren su Shekaru suke zargin hedkwatar jam’iyyar da marawa Kwankwaso baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG