Kakakin hukumar 'yansanda a Jihar Gombe DSP Attajiri ya tabbatar da harin yayin da wakilin Muryar Amurka ya zanta da shi game da lamarin. Ya ce 'yansandan sun yi nasarar fatartakar maharan. Ya ce babu wanda ya mutu sai dan sanda daya da ya samu rauni wanda tuni suka kaishi asibiti. Ya musanta batun cewa jami'in ya rasa ransa. Kawo yanzu inji jami'in 'yansandan, babu wanda aka kama sai dai suna cigaba da bincike.
Sai dai a fira da wakilinmu ya yi da mazauna garin wani ya ce dan sanda daya mai suna Boka ya rasa ransa a harin. Da aka tambayeshi ko mutanen garin wani ya ji ciwo sai ya ce kawo lokacin da ya ke magana babu labarin cewa wani a garin ya ji ciwo. Ya ce cikin garin babu matsala domin komi ya dawo dai-dai. 'Yansanda sun bazu cikin garin lamarin da ya bada alama an kara jami'an tsaro.
Mutanen garin Kumo sun kwana cikin fargaba domin hare-haren da karar pashe-pashe sun dauki fiye da awa daya ana jinsu lamarin da ya firgita kowa musamman wadanda gidajensu na kusa da ofishin 'yansandan.
Ga rahoton wakilinmu Abdulwahab Mohammed.