Britaniya ta ce ta dauki matakin ne domin ta dakile matsalar bakin haure da masu zuwa ziyara amma kuma sai su makale a kasar. Wannan lamarin ya dade yana ci ma 'yan siyasar kasar tuwo a kwarya.
Domin samun cikakken dalili abokiyar aiki Halima ta zanta da wakilin Murya Amurka a birnin London.A nashi bayanin ya ce matsala ce da ta zama wa kasar kamar makalewar kayar kifi a wuya. Ya ce matsayin ya samo asali ne tun daga gwamnatin Leba da ta shude amma sai a wannan karon ne sakatariyar cikin gida mai kula da shige da ficen baki ta kawo wannan shawarar da za'a fara da kasashe shida a zaman gwajin dafi. Kasashen ko su ne Pakistan, India, Nigeria, Bangladesh, Ghana, da Sri Lanka. Idan shawarar ta zama doka zata fara aiki ne daga watan Nuwamba mai zuwa. Idan ta yi tasiri sai a fadadata kan sauran wasu kasashe.
Kodayake shawara ce sakatariyar ta mika wa 'yan majalisa akwai harsashen cewa idan 'yan majalisa suka dawo daga hutunsu zasu iya kada kuri'ar amincewa ta zama doka. To sai dai gwamnatocin kasashen da aka ambata dokar cikin shawarar basu ce komi ba tukunna.
Ga karin bayani a wannan rahoton.