Kimanin mutane dubu daya da dari biyar da hamsin suka rasa gidaje da wuraren kasuwancinsu a garin na Bama, a lokacin da wadannan 'yan bindiga na kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram suka far ma garin a ranar 7 ga watan Afrilu, har aka zub da jini mai yawa.
Tun daga lokacin ne gwamna Kashim Shettima na Jihar ya kafa Kwamiti karkashin jagorancin Alhaji Usman Iidda Shuwa domin binciko irin hasarar da aka yi da wadanda suka yi hasarar da nufin ba su irin taimakon da za a iya.
A bayan da kwamitin ya mika rahotonsa, gwamna Shettima yayi zaman gaggawa da majalisar zartaswarsa, inda suka amince da cire Naira miliyan 100 domin tallafawa mutanen na garin Bama.
Wakilin sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, ya aiko da cikakken rahoto.