Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya, shi ya fadi hakan ta bakin wakilinsa ministan ayyuka Mike Onelememen, a wani taron Cibiyar Samar Da Ayyukan Yi Ga 'Yan Najeriya a Lagos. Wannan shi ne karo na biyar da cibiyar take gudanar da irin wannan taron lacca a kan "Hanyoyin Inganta Mulki Mai Tasiri ga 'Yan Najeriya."
Shugaba Jonathan ya ce idan har dan Najeriya zai ki bin dokar kasa, to kuwa lallai yana yaudarar kansa ne idan har yana tsammanin kasa zata samu ci gaba.
Tsohon shugaban soja, Janar Abdulsalami Abubakar, da tsohon ministan ayyuka Dr. Hassan Lawal, wanda ya wakilci Janar Muhammadu Buhari a wurin wannan taron, duk sun yi magana kan abubuwan da suek ganin zai kawo ci gaban kasa.
Wakilinmu Ladan Ibrahim Ayawa, ya fara da tambayar Janar Abdulsalami Abubakar, ko yana ganin wannan taron zai yi wata fa'ida, ganin cewa ba yau aka saba gudanar da irin wadannann tarurruka ba, amma kuma har yanzu ba ta canja zani ba? Sai tsohon janar din ya kada baki yana cewa.