Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Siyasa Sunyi Korafi a Kan Tsadar Fom Din Tsayawa Takara


Wasu 'yan siysa sunce bai cancanta ba a tsawwala kudaden sayen fom din tsayawa takarar zabe mai zuwa.

Ana nan ana ta shirye-shiryen zaben shekarar 2015. Wakilin muryar amurka, Mustapha Nasiru Batsari, ya bada rahoton akan farashen kudaden fom din tsayawa takarar zabe, tun daga kujerar shugaban kasa zuwa kansila na jami’yyun PDP da kuma jam’iyyar adawa ta APC.

Sanata Ibrahim Musa na daya daga cikin ‘yan takarar da suka yanki tiketin neman mukamin Gwamna a jam’iyyar APC a jihar Neja, shima ya koka da kudin sayen fom din ya kuma fadi cewa tsawwala kudin zai iya hana wasu da suka cancanta tsayawa takarar.

Haka zalika Shi ma sakataren yada labaran jam’iyyar adawa ta APC a jihar Neja, Mr. Jonathan Batsa ya fadi cewa kudaden sayen fom din sun yi yawa.

Ga cikakkiyar hirar da Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG