Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Neja Zai Yi Takarar Sanata


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Gwamnan Jihar Neja zai nemi mukamin sanata domin shiga majalisar dattawa

Zai wakilci yankin gabashin jihar tasa, kujerar da marigayi sanata Dahiru Kuta ya bari.

Yanzu Dr, Zabayi ne ke rike da kujerar sakamakon zaben cike gurbi da aka gudanar.

Alhaji Hamisu Jankaro shi ne shugaban kungiyar dake fafitikan ganin gwamnan ya haye kan kujerar da zara ya kammala wa'adin mulkinsa.

Bayan sun sayawa gwamnan tikitin tsayawa zaben Jankaro yace suna son gwamnan ya wakilcesu a majalisar dattawan kasar. Alamu na nuwa gwamnan yana samun goyon bayan jam'iyyar PDP.

Alhaji Muhammed Gambo shugaban PDP a yankin yace tsari ne na jam'iyyar. Yace shi Dr Zabayi dan jam'iyya ne kuma yana biyyaya da ita sabili da haka zai barwa gwamnan ya maye gurbinsa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG