Duk da raderadin da ake yi na fitar Aminu Waziri Tambuwal daga PDP har yanzu bai bayyana ba a hukumance.
Amma halartar taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a Sokoto da yayi tare da jawabin gwamnan jihar Aliyu Magatakardan Wamakko sun sa ana ganin ya koma APC din ko. Yace idon kowa na kan shi Aminu Tambuwal. Yace tun ranar da aka kafa jam'iyyar APC tare dashi aka kafata. Babu abun da suke yi a jam'iyyar ba tare da shi ba. Amma su suka bashi shawara ya tsaya cikin PDP tukunna domin ya kare masu bakin wuta.
Amma ranar wanka ba'a boye cibi. Gwamna Wamakko yace yanzu an kawo ranar wanka sabili da haka dole Aminu Tambuwal ya fito kowa ya ganshi.
Du da yake an cigaba da taron ne a asirance daga karshe wakilin Muryar Amurka ya nemi ya ji ta bakin Aminu Tambuwal akan matsayinsa amma yaki ya zanta dashi. Saidai jami'in watsa labarai na kakakin Imam Imam ya fitar da wata sanarwa inda yace jam'iyyar PDP na gudanar da wani taro a Sokoto amma bata gayyaci kakakin majalisar ba a matsayinsa na shugaba kuma jigo a jam'iyyar. Yace gwamna Wamakko ne ya bashi goron gayyata zuwa taron na APC a matsayinsu na abokan siyasa shi yasa ya halarci taron.
Gwamna Wamakko yace makasudin taron shi ne tattauna yadda za'a samarda 'yan takara daban daban na jam'iyyar a cikin ruwan sanyi da sasantawa domin tunkarar zabe mai zuwa. Yace shi bashi da dan takara sai wadanda 'yan jam'iyyar suka nada.
Sakataren APC na jihar Sokoto Aminu Bello ACY yace sun yi taro ne domin a samu a fitar da 'yan takara.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.