Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Siyasa Sun Bukaci Amurka Ta Shawo Kan CEDEAO Don Sassauta Takunkumin Da Ta Kakaba Wa Nijar


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Wasu ‘yan siyasa daga jam’iyyar Democrat a Amurka sun bukaci sakataren harkokin wajen Amurka da jakadiyar Amurka a Majalisa Dinkin Duniya su yi amfani da damar babban taron Majalisar Dinkin Duniya don tuntubar shugabanin kasashen CEDEAO kan bukatar sassauta takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar.

Wadannan ‘yan siyasa mambobin Congres da suka hada da Sara Jacobs, da Sydney Kamlagor Dove, da Ilhan Omar, da James P. McGovern, da kuma Joaquin Castro, a wasikar da suka aike wa sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Dunia Linda Thomas Grenfield, sun bayyana cewa takunkumin da ECOWAS ta kakaba wa Nijar da kuma matakan da sojojin juyin mulki suka dauka sun takaita hanyoyin samar da kayan abinci da magunguna.

Haka kuma masu ayyukan ci gaba da masu ayyukan agaji basa samun sukunin cire kudaden da suka dace daga bankunan kasuwancin da ke kasar, lamarin da ke haddasa cikas wajen daukar dawainiyar ayyukan ci gaban da aka kudirta.

‘Yan majalissar sun kara da cewa kafin a yi juyin mulki an kyasta mutane million 4.3 na cikin halin bukatar agaji, haka kuma a tsakiyar watan Agustan da ya gabata an gano mutane million 3.3 da ke cikin halin matsanancin karancin abinci kuma ta yiwu wasu da dama su fada matsanancin halin rashin abinci sakamakon takunkunmin da aka kakaba a yayin da jami’an agaji ke cewa guzurin abincin da ke a jiye a halin yanzu ba zai cimma bukatun mutane milion 1.2 ba, watakila ya kai karshen watan Satumba.

Sannan kudaden da ke hannu a yanzu domin ayyukan agaji mai yiwu su kare a watan Nuwamban 2023, abin da ka iya jefa mutane sama da million 1 cikin halin rashin samun tallafin da suke bukata.

La’akari da tarin matsalolin da aka shiga a Nijar da ka iya shafar rayuwar al’umma ya sa wadannan ‘yan majalisa su biyar kiran gwamnatin Biden ta shawo kan shugabanin CEDEAO su sassauta takunkumin da suka kakaba don samar da hanyoyin shigar da kayan agaji, haka kuma ya zama wajibi kungiyar ta kasashen yammacin Afrika ta yi la’akari da ka’idar nan da ke cewa kada a dauki matakin cutarwa a irin wannan yanayi.

Shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula ta ROADD Dambaji Son Allah, ya yaba da wannan yunkuri, koda yake a ganinsa akwai bukatar daukar wasu matakai na dabam.

‘Yan majalisar sun yi godiya kan jajircewar gwamnatin Amurka game da maganar mayar da al’amuran mulkin Nijar a hannun farar hula ta hanyar goyon bayan da take bai wa kungiyar ECOWAS a yunkurin da ta sa gaba.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Wasu ‘Yan Siyasa Sun Bukaci Amurka Ta Shawo Kan CEDEAO Don Sassauta Takunkumin Da Ta Kakaba Wa Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG