Ƙwararru da masana harkokin tarbiyya da kuma ɗabi’a sun fito fili sun nuna cewa ya na da muhimmanci gwamnatin tarayya da kuma ta jihar Katsina su ɗauki matakan kawar da tunani mara kyau a zukatan ɗalibai sama da ɗari huɗu da ‘yan bindiga suka sace daga makarantar sakandaren kimiya ta garin Ƙanƙara a Jihar Katsina, domin tabbatar da cewa wannan tashin hankalin bai shafi rayuwarsu ba a nan gaba.
Malam Shehu Ɗandaura, ƙwararre ne a kan harkokin tarbiyya, Ɗa’a, da zamantakewa ta tunanin mutane, ya ce abinda ya kamata a yi kafin a maida su gidajensu ko kuma lokacin da aka kai su, shi ne a basu kwarin gwiwa da taimakon shawarwari don da yawa daga cikinsu rayuwarsu ta canza, ta yiwu wani ma yanzu ya na kallon bindiga a matsayin wani abin alfahari tunda a bakin bindiga aka sace su, hakan kuma na iya kawo rashin imani a rayuwa.
Dr. Kabir Mustapha, babban sakatare a ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Katsina, shi kuma cewa ya yi matakin farko da gwamnati ta ɗauka, na duba lafiyar daliban a sansanin mahajjata da sake musu tufafi da aka yi ya sa sun dan koma cikin hayyacinsu kuma zai ɗan kwantar musu da hankali.
Ya kara da cewa wani abun damuwa shi ne fargaban da daliban zasu fuskanta a lokacin da zasu koma makaranta tunda yanzu su na hutu, da yawansu za su dinga gani kamar wani abu zai same su. Amma Dr. Mustapha ya ce su na ƙoƙarin ganin sun tura ƙwararru a fannin ɗabi’a don su dinga basu shawarwari su na kwantar musu da hankali domin raba su da wani tunani mara kyau.
Saurari rahoton Umar Faruk Musa:
Karin bayani akan: Boko Haram, sojoji, Buhari, da jihar Katsina.