Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Hudu Daga Cikin Sauran Daliban Makarantar Sakandaren Yawuri Daga Hannun ‘Yan Bindiga


An sako wasu daga cikin daliban makarantar Yawuri
An sako wasu daga cikin daliban makarantar Yawuri

Samun ‘yantar da dalibai mata hudu daga cikin sauran goma sha daya ‘yan makarantar birnin Yauri da suka rage a hannun masu garkuwa da mutane, alama ce da ke nuna ana iya kubutar da sauran daliban.

Munira Bala Ngadski da Sarah Musa, na daga cikin iyayen daliban hudu da suka shaki iskar ‘yanci, sun bayyana farin cikinsu tare da yin godiya ga Allah. Sai dai a cewar Sarah Musa har yanzu suna cike da juyayi a kan sauran dalibai bakwai da har yanzu ke cikin daji a hannun ‘yan bindiga kusan shekara biyu.

Ta kara da cewa wasu daga cikinsu, ko da Allah ya yi fitowarsu ba zasu taras da mahaifansu ba saboda bakin cikin rashin yaran ya kashesu, kamar yadda Munira Ngadski ta ce ita ma Allah ne ya sa tana da sauran kwana har ta ga fitowar diyar ta.

A ranar 17 ga watan Yuni na shekarar 2021 ne masu garkuwa da mutane suka afka makarantar sakandaren gwamnatin tarayya da ke birnin Yauri a jihar Kebbi suka sace dalibai, da malamai, da wasu ma’aikatan makarantar.

An sako wasu daga cikin daliban makarantar Yawuri
An sako wasu daga cikin daliban makarantar Yawuri

Bayan da gwamnati ta ceto wasu daga cikin daliban da aka sace har sau biyo, an samu ragowar dalibai mata goma sha daya a hannun ‘yan bindiga.

Iyayen yaran sun yi ta jerangiya tare da neman taimakon hukumomi don ceto sauran daliban amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, har sai da suka kaddamar da neman taimakon kudin biyan fansa daga jama'a.

Salim Ka'oje, shi ne ya jagoranci wannan fafutuka. Ya fadi cewa sun saida kaddarori da gonakinsu suka hada da kudin da jama’a suka tattara don ceto yaran.

Ya kara da cewa wani kwamiti mai mambobi biyar wanda ya jagoranta ne ya yi shahada tare da shiga dajin don neman ceto daliban.

Duk da yake gwamnatin Kebbi ba ta taka wata muhimmiyar rawa wajen ceto daliban ba, a yanzu dai gwamnatin ce ke daukar nauyin kula da lafiyar daliban da suka shafe shakara biyu a dawa, a cewar shugaban kungiyar iyayen yaran Salim Argungu.

Nan take dai gwamnatin jihar Kebbi bata ce komai ba game da batun.

A halin da ake ciki, Salim ya ce suna ci gaba da fafutukar ganin an sako sauran ‘yan matan bakwai da suka rage a hannun ‘yan bindiga.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG