Wani ƙarin ɗan sanda ɗaya kuma ya sami rauni yayin da su ma wasu ƴan tireda da ke gudanar da kasuwanci a gefen titi da ma wasu masu wucewa suka sami raunuka.
Kwamishinan ƴan sandan birnin Abuja, Sadiq Bello ya tabbatarwa Muryar Amurka aukuwar wannan al'amari.
Kakakin hedikwatar rundunar ƴan sandan Najeriya, Alhaji Moshood Jimoh ya bayyana cewa wadannan ƴan sanda bakwai da ƴan fashi suka kashe sun gamu da ajalinsu ne suna bautawa kasarsu, kuma tuni aka ƙaddamar da bincike don kamo waɗanda suka tafka wannan aika-aikan.
Mai sharhi kan sha'anin tsaro, Mallam Kabiru Adamu ya bayyana cewa, wannan kisa na ƴan sanda abin mamaki ne musamman ganin yawansu amma suka gaza kare kansu,
A matsayinsa na masanin tsaro yana zargin ko dai ƴan fashi ko kuma ƴan bindiga masu neman makamai suka aikata harin. Koda yake bincike ne kadai zai tabbatar da abin da ya faru.
Kawo yanzu an ƙara yawan jami'an tsaro a yankin da wannan al'amari ya faru, kasancewar dama yankin Galadimawa ya daɗe yana fuskantar miyagun mutane.
Facebook Forum