Ita rundunar sojin kasar ta fada cewa can baya ta cafke wasu jami'anta biyu akan zargin tseguntawa 'yan Boko Haram wasu bayyanan sirri.
Kakakin sojojin Najeriya Janar Rabe Abubakar yace zasu cigaba da kama sojoji bata gari dake cikinsu. Yace zasu yi iyakar kokarinsu su yi yakin tsakaninsu da Allah har sai sun ga bayan ta'adancin 'yan Boko Haram. Duk wadanda suke ba 'yan ta'adan goyon baya Allah zai tona asirinsu. Ya kara da cewa duk wadanda suke da hannu a wannan laifin ko a daureshi ko kuma a kasheshi.
Masana harkokin tsaro irinsu tsohon jami'in leken asiri a rundunar sojojin Najeriya Aliko Harun ya sa ayar tambaya dangane da harin baya bayan nan da ya rutsa da kwamandan mayakan tankokin yaki na bataliya ta 272 a jihar Borno Leftanar Kanar Abu Ali. Yace biri yayi kama da mutum saboda Kanar Irabor ya fada cewa akwai sojojin da suka baiwa Boko Haram bayyanan sirri. Yace mutuwar Abu Ali ba banza ba ce.
Shi ma Kwamanda Tijjani Baba Gamawa yace cin amanar kasa ne kwarmata bayyanan sirri ga abokan gaba. Bai kamata jami'in tsaro ya hada baki da masu kawo fitina ba. Yace amma idan an bi sawun barawo to a bi na mabi sawu. Yace muddin aka bar jami'an tsaro suka dade a wuri guda ba tare da canza masu wurin aiki ba to irin wannan lamarin babu wuya ya faru.
Ga rahoton Hassana Maina Kaina da karin bayani.