A kwanakin baya rundunar sojan Najeriya tace ta kame wasu jami’anta guda biyu da laifin tseguntawa mayakan Boko Haram bayanan sirri. Hakan yasa wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina, ya tuntubi kakakin rundunar sojan Najeriya, Janal Rabe Abubakar.
Kakakin yace a baya sun kame wasu jami’ansu haka kuma zasu ci gaba da bincike domin gano duk wani jami’in dake taimakawa ‘yan Boko Haram. Rundunar soja dai ta mayar da hankalinta don ganin ta sami nasara akan wajen gano sauran jami’anta dake da hannu domin a hukuntasu.
Sai dai masana tsaro na dasa ayar tambaya dangane da harin baya bayan nan da yayi sanadiyar rasuwar kwamandan mayakan tankokin yaki na Bataliya ta 272 a jihar Borno, Laftanar Kanar Mohammad Abu Ali. A cewar Aliko El-Rashid Harun, Biri yayi kama da mutum akan abin da ya faru a kwanakin baya domin tabbas akwai sojojin da suke baiwa Boko Haram bayanan sirri.
Cin amanar kasa ne a kwarmata bayanan sirri ga abokan gaba – inji Ahmed Tijjani Baba Gamawa, ya ci gaba da cewa bai kamata ba jami’in tsaro ya hada baki da mutanen dake kawo fituna a kasa. Ya kuma bayar da shawarar a rinka yiwa jami’an tsaron canjin gurin aiki, domin da zarar an bar ma’aikaci a guri ya dade zai iya shiga cikin wasu harkokin da basu kamata ba.
Domin karin bayani.