Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Suna Yin Aikin Yan Sanda


Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Buratai, yana kaddamar da babura na sojoji
Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Buratai, yana kaddamar da babura na sojoji

Masana tsaro na ganin aikace aikacen da rundunar sojan Najeriya ke yi a jihohin Najeriyar abu ne dake takura karfin sojojin.

Akwai ayyukan tsaron cikin gida masu yawa da yakamata ace jami’an ‘yan sanda ne ke yi a Najeriya, amma sojoji ne ke gudanarwa. Kama daga Operation Lafiya Dole a shiyyar Arewa maso Gabas da Operatin Sharar Daji a shiyyar Arewa ta Yamma da Operation A Watse a Kudu ta Yamma da kuma yankin Niger Delta inda sojojin ke gudanar da wasu ayyuka har guda Hudu ciki har da Operation Delta Safe.

Ire iren wadannan ayyuka da sojojin ke yi wadanda ake musu take Operation sun kai har 15 a jihohin Najeriya 32.

Wakilin Muryar Amurka a Abuja Hassan Maina Kaina, ya tambayi kakakin rundunar sojojin Najeriya, Kanal Sani Usman Kuka Sheka shin ko wadannan ayyukan basa yiwa sojojin yawa? Kanal Kuka Sheka, yace baza a taba cewa abu yafi karfin sojojin Najeriya ba kasancewar duk inda aka duba nasara ce kawai ake samu.

Shugaban rundunar sojojin Najeriya Lutanal Janal Tukur Buratai, ya tabbatar da cewar sojoji na yin bakin kokarinsu wajen kare muradun kasa baki daya.

Shi kuwa tsohon Hafsa a rundunar sojan Najeriya, Aliko El-Rashid Harun, na ganin cewa ayyukan da sojojin ke yi a fadin jihohin Najeriya sunyi yawa, ya kuma shawarci rundunar sojan da ta rinka mikawa wasu ayyuka ga ‘yan sandan kasar.

Sai dai kuma Kanal Aminu Isa Kwantagora, na ganin rashin karfafa karfin ‘yan sanda a Najeriya shine yayi sanadiyar wasu ayyuka suka koma hannun sojoji.

Mataimakin Sufeta Janal na Yan sanda mai murabus Ibrahim Baba Ahmad, yace ayyukan da ‘yan sanda ke yi yafi karfinsu a Najeriya, akwai ayyukan da yakamata su yi akwai kuma wanda bai kamata ba, haka kuma suna da hurumin gayyato sojoji idan suka kasa gama wani aiki. Ya kuma ce maganar an dauki aikin ‘yan sanda an daura sojoji ba haka maganar ta ke ba.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG