Rundunar sojin Masar ta ce an fafata jiya Asabar tsakanin wasu da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne da sojojin gwamnati, a wani wurin duba ababen hawa da ke yankin Ruwan Sinai.
Wani mai magana da yawun sojin kasar, ya fadawa kamfanin Dillancin labaru na AFP a wani rubutaccen bayani cewa, an hallaka mayaka bakwai a wani harin da aka kai a Sinai mai fama da tashin hankali, yayin da sojoji 15 ake tunanin ko dai sun mutu ko sun ji rauni.
Tamer El-Refai, Mai magana da yawun sojojin ya fada a cikin sanarwar cewa, “jami’in soja daya da kuma wasu 14 sun mutu ko sun ji raunuka,” amma ya gaza bayyana adadin wadanda suka mutu.
El-Refai ya ce jami’an tsaro za su bi bayan “dun inda ‘yan ta’adda suke domin su kawar da su.”
Facebook Forum