Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Fada Ya Halaka Mutum 69 a Kamaru

Wani wuri da aka kona a yankin da ke kusa da garin Buea a kudu maso yammacin kasar Kamaru da ke amfani da harshen Ingilishi. Ranar 4 ga watan Oktoba, 2018.
Wani wuri da aka kona a yankin da ke kusa da garin Buea a kudu maso yammacin kasar Kamaru da ke amfani da harshen Ingilishi. Ranar 4 ga watan Oktoba, 2018.

A wannan lokaci ne, mayakan ‘yan aware da ke dauke da makamai, suka ayyana rufe daukacin yankunan har na tsawon kwanaki 10, inda suka haramta gudanar da ayyuka da dama har sai ranar 14 ga watan Fabrairu.

Wani sabon fada da ya barke a yankin da ke amfani da harshen Ingilishi a kasar Kamaru, ya yi sanadin mutuwar mutum 69.

A wannan yankin ne har ila yau, mayakan ‘yan aware suka ba al’umarsa umurnin su zauna a gidajensu, yayin da kasar ke shirin bikin ranar matasa.

Bikin wanda za a yi a ranar 11 ga watan Fabrairu, na zuwa ne a daidai ranar da ake tunawa da lokacin da aka yi zaben raba- gardama a shekarar 1961, wato lokacin da ‘yan awaren suke nuni da cewa, lokacin ne da aka mika yankinsu da ke amfani da harshen Ingilishi ga yankin da ke amfani da harshen Faransanci.

Tun dai a ranar Talatar da ta gabata, ake ta gwabza fada a garuruwan Limbe, Beau, Mutengene, Kumba da ke amfani da harshen Ingilishi, da kuma wasu garuruwa da ke arewa maso gabashin kasar.

“Da safiyar yau, dakarun Kamaru suka kawo mutum 11 da suka ji rauni, kuma ba za mu iya kula da su ba, saboda muna da karancin ma’aikata, sannan babu magunguna.” Inji Frederick Mengoli, ma’aikacin jinya a wani asibiti mai zaman kansa a garin Limbe.

A wannan lokaci ne, mayakan ‘yan aware da ke dauke da makamai, suka ayyana rufe daukacin yankunan har na tsawon kwanaki 10, inda suka haramta gudanar da ayyuka da dama har sai ranar 14 ga watan Fabrairu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG